Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani, wanda ke jagorantar tawagar Iran a birnin Vienna, ya jaddada cewa, burin farko na Iran a zaman shawarwarin shi ne soke dukkanin takunkumin da aka kakaba mata.
Sabon zagayen tattaunawar zai zama irinsa na bakwai kuma na farko bayan da shugaban Iran mai ci a yanzu Ibrahim Raisi ya hau kujerar mulki a watan Agustan 2021.
Wakilin kasar Rasha a tattaunawar Mikhail Ulyanov ya bayyana cewa, "Muna da kuduri mai kyau ta fuskar ganin cewa an samun nasarar kammala shawarwarin.
Daga watan Afrilu zuwa watan Yunin bana, Vienna ta karbi bakuncin zaman shawarwari 6 a karkashin inuwar kungiyar Tarayyar Turai, domin ceto yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukiliyar Iran, bisa la’akari da ficewar Amurka daga cikinta a shekarar 2018 a lokacin mulkin tsohon shugabanta Donald Trump.
Trump, wanda ya sanya takunkumi mai zafi a bangaren Iran, don mayar da martani ta hanyar rage alkawurran da ya dauka a cikin yarjejeniyar daga 2019.
342/